Arewahausatv latest news

Labaran duniya

Tarihin malam gajere Dan iyan kano part 1

DAN-IYAN KANO MALAM GAJERE

BABI NA DAYA SIYASA DA MULKI

Wannan babi da muka kira Siyasa da Mulki, muna fatan yin bayani ne a kan asali da yaki, da siyasa da yadda hakan ya tabbatar da mulki. Farkon bayanan mu za su kasance da fadi amma daga karshe za mu tsuke su a kan bayanin matsayin Dan- Iyan Kano Muhammadu Malam Gajere da irin rawar da ya taka musamman tsakanin shekara ta 1893 zuwa shekara ta 1902. Haka kuma za mu kalli matsayi da asalin zuriyar sa. Don haka za mu yi bayanai bisa doron wadannan take:-

1. Sullibawa kafin jihadi

2. Sarkin Kano Ibrahim Dabo

3. Yusufawa da Tukurawa

4. Tarewa a Unguwar Daneji

5. Sulhu da Turawa

6. Zuri’ar Malam Gajere a yau.

1. Sullubawa kafin Jihadi Marigayi Wazirin Sakkwato Malam Junaidu wanda ya ke Malami ne kuma masanin tarihi, ya yi bayani a shekara ta 1985 a wani shiri na radio Kaduna cewa Fulani sun samo asali ne daga auren da aka yi tsakanin wani Balarabe da wata Bayahudiya. Ta wannan tsatso ne Allah Ya kaddari samuwar kabilar Fulani. Daga bayma suka yawaita a nahiyar Afrika da sunaye daban-daban a dalilin wajen zaman su ko shugabancinsu. Wannan bayani na Malam (Dr.) Junaidu na nuna cewa Fulani dai dangin Larabawa da Yahudawa ne. Su kuma daman Larabawa da Yahudawa asalinsu guda ne. Dukkanin su, Annabi Ibrahim(AS) ne kakan su. Wasu masu nazarin tarihin sun amince da cewa Larabawan da suka watsu a duniya bayan manzo mai tsira da aminci ya yi hudubar ban kwana a shekara ta 693AD sun hadu da sauran jinsuna na duniya, kuma sun haifar da wasu al’ummai. Wadannan ma su nazari sun ce Fulani sun fito ne daga tsatson wani Balarabe da ya zauna a arewacin Afrika wanda asalinsa Arabiya. A dunkule dai wadannan bayanai guda biyu na nuni da cewa Fulani dai asalin su Larabawa ne. Idan aka yi la’akari da kamannin su za a iya amincewa. Wasu marubuta tarihi Stride da Ifeka (1971) sun yi bayani cewa Fulani na cikin kabilun Senegal da Gambia (Sene-Gambia) wanda ke yammacin Afrika. Sun ce Fulani sun yi auratayya da kabilun wajen kamar kabilar Mandika. Haka kuma sun yi auratayya da kabilun Arewacin Afrika kamar Buzaye da Auzunawa. Dukkanin wadannan bayanai za su iya hadewa domin su Fulani ma su yawace-yawace ne kuma zai kasance a zagayan su ne, su ka gangara yammacin Afrika har suka yi kaka-gida a can. Daga can ne kuma su ka kara yaduwa a sauran bangarorin yammacin Afrikan, ciki har da kasar Hausa.

Tarihi ya tabbatar da cewa sai a shekara ta 1591AD watau bayan rushewar babbar Daular nan ta Songhai ne Fulani suka sami damar ketara ko’ina a Afrika ta yamma domin kafin wannan lokaci harajin zirga-zirga da daular ta sanya ya tauye mu su tafiye-tafiye a fadin kasashen yammacin Afrika. Wannan dama ta ba su damar tafiya nesa da kusa. Hakan kuma ta taimaka wajan yaduwar su da kaka gidansu a wurare. Mafi yawancin lokaci ana karkasa Fulani zuwa kashi biyu rak. Masu zaune a gari da kuma masu zaman jeji da gonaki. Wadanda ke zaune waje daya (a gari) sun sanya karatu ne a gaba. Duk da haka suna kiwo da noma. Wadansu na kai shanun su gona ko jeji wajen ‘yan uwan su na can, wasu kuma na yin kiwon su a gari. Wannnan na nuni da cikakkiyar alakar da ke tsakanin fulanin da ke cikin gari da wadanda ke jeji. Alakar su da zumuncin su na nan, illa dai kowa akwai abinda ya fi sanyawa a gaba. Sunayen kabilun Fulani ya samu ne a dalilin wajan zaman su ko shugabancin su. Misali fulanin da ake kira Gyanawa, an ce sunan shugaban su Malam Gyane. Fulanin da ake kira Yolawa a Kano, ance asalin su daga Yola ne ta kasar Adamawa. Haka duk sauran fulanin, ko dai wajen zama ko shugabanci. Fulani a matsayin su na jinsi na daga farkon wadanda suka rungumi addinin Musulunci a Afrika. Haka kuma suka dage wajen neman ilimi da yada shi. Wannan ta sanya suka haifar da manyan Malamai a cikin su wadanda kamar yadda za mu karanta nan gaba suka yunkura don yin jihadin daukaka Kalmar Allah. Suka kakkafa manyan masarautu karkashin babbar daular de ba a samu irin ta ba, kafin wannan yunkuri da suka va karkashin shugaban su Shehu Usman Dan Fodio. Sullibawa na daga cikin sanannu a kabilun Fulani, Sun dade kwarai a kasar Hausa musamman a kasashen Arewa maso yamma watau Sokoto da zagayenta, da kasar Katsina da kuma Kano. Sun samu sunan su daga sunan shugabansu kuma kakan su, Silsilo. Tun ana cewa silsilbe har aka dinga kiran su sullibawa. Kamar sauran kabilun Fulani, sullibawa kashi biyu ne, akwai na gari wadanda ke zaune suna karatu da karantarwa, akwai kuma masu kiwo a gona ko jeji. Misalin dadewar wannan kabila a kasar Hausa za mu fahimce shi ne daga wata tattaunawa da mawallafin ya yi da wata bafulatana mai kiwo da kuma tallar nono da mai. Bayan an gaisa da yaran fulatanci, sai aka ci gaba da bayanai a yaran sai ta ce, “Ai ni basullubiya ce. Kakana ne kawai yake jin fulatanci amma mu sai yaran Hausa, duk da cewa kome irin na Fulani mu ke yi. Dukkanin al’adun mu baki daya. Dadewar kabilar mu tare da Hausawa ne ya jawo haka”. Sai mawallafin yace, “Ai duk kanwar ja ce. Ku kun yi sa’a akwai a cikin ku, ma su yarawa, ai mu babu, dan wanda ki ka ji na yara, tsinta na yi. Ku don kuna karkara ne, amma mu a nan birni ina! Bayan harshen Hausan ma, akwai tasirin Turanci da Larabci. Amma kin san duk ta’adar mu baki daya ta Fulani ce, har ma

idan mun yi wani abin wanda ya saba sai a kalle mu, a ce, sai ka ce ba Bafulatani ba”. Wannan tatttaunawa ta fito da abubuwa kamar haka:- Cewa sullibawa na daga kabilun Fulani. Cewa sun dade a kasar Hausa. Cewa suna rike da al’adunsu na Fulani duk da cewa sun yi shekaru da yawan gaske a kasar Hausa. Cewa Fulani, mutane ne masu tunkaho da alfahari da asalin su da al’adunsu. Kuma sun fi kaunar a gan su kullum a matsayin Fulani. Cewa yaran Hausa ya sha gaban yaran Fulatanci. Sanan nan shugaban sullibawa wanda tarihi ya tabbatar a Kano shi ne Malam Jamo. Haka kuma akwai ‘yan uwan sa irin su malam Dahiru da Malam Ibrahim Dabo. Kamar yadda za mu karanta nan gaba lokacin da malaman Fulani na Kano suka yunkura don koyi da shehunsu, Usman Dan Fodio na yakin jihadi a Kano, sullibawa sun shiga al’amarin ne karkashin shugaban su Malam Jamo. An yi bayanin sa, a matsayin dattijo mai ilimi da takawa da kuma rungumar ‘yan uwa da sauran jama’a. Kafin wannan yunkuri sullibawa na zaune a kasar Kano a birni da karkara. Sun fi yawa a kasashen kiru da Kanwa da Madobi. Haka kuma kamar yadda mu ka yi bayani masu bidar ilimi kuma Malamai a cikin birnin Kano. Masallacin da ke unguwar Galadanci ta cikin birnin Kano, shi ne masallacin da sullibawa suka gina kamar yadda idan aka je kowane sansani na Fulani a birin Kano za a ishe masallacin su na asali.

(( Mu hadu a kashi na biyu ))

Leave a Reply