Arewahausatv latest news

Labaran duniya

Tarihin malam gajere dan iyan kano part 2

(( Kashi na biyu )) ci gaban kashi na daya

Sullibawa ba su yi alaka da sarakunan Hausa ba a Kan. Suna waje daya suna ta karatu da karantarwa. Suna amfani da yaran Larabci da na Fulatanci wajen bayar da karatu da yin wa’azi. Sun tara malamai da yawa kamar yadda sauran jinsin Fulani musamman wadanda ke cikin birni suka yi. Duk da haka suna ci gaba da kiwo da noma kamar yadda mu ka ambata a baya. Don haka za a iya yin dalla-dalla ace sullibawan Kano kafin jihadi sun kasance:- Wadanda suka sanya karatu da karantarwa kawai a gabansu. Don tafiyar da rayuwa suna kiwo da noma. Babu ruwan su da harkar mulki.

• Wannan yanayi ya sanya sun tara ilimi mai yawa. Babu mamaki a ce suna ta ganin sarakuna da sauran shugabanni a kan karkataciyyar turba domin shi ilimi ya dinga bambance daidai da kishiyar haka. Jahilci ne yakan gwama biyun baki daya. Sarkin Kano Ibrahim Dabo Kafin mu yi bayanin yadda Malam Ibrahim Dabo ya zamo sarkin Kano da irin canje-canjen da ya kawo wajen tafiyar da mulki da yadda hakan ya tabbatar da zuriyarsa da ake wa lakabi da sulli6awan Dabo a mulkin Kano, ya zamo wajibi mu yi bayanin jihadin da aka yi a kasar Hausa da dalilan yin sa da abin da ya haifar. Kamar yadda tarihi ya tabbatar musulunci ya dade da zuwa kasar Hausa. An fara gabatar da shi ne ta hanyar

mu’amala da cinikayya tsakanin arewaci da yammacin Afrika. ‘Yan kasuwa da sauran jama’ar da ke zuwa daga kasashen arewa kamar Turafulus (Libya) da Misra. (Egypt) da dai sauran kasashen arewacin Afrika na nesa kwarai da kasar Hausa da kuma sauran kasashe kamar Timbuktu da Agadas da Gao da sauransu, ne suka zo da addinin musulunci. Tun suna yi ana ganinsu, ana sha’awa har aka dinga koyi da kuma shiga addinin. Shi kuma addinin musulunci yana tafiya ne da koyarwa da koyo, don haka sai ilimin addinin da kuma rubutu da karatu ya fara yaduwa. Addinin ya samu gata a kasar Hausa lokacin da sarakuna suka karbe shi. Misali a Kano, lokacin sarkin Kano Tsamiya (1307-1343AD) da kuma dan sa Ali Yaji (1349 – 1385AD) addinin musulunci ya samu yaduwa. Sarakunan sun:- Rushe wuraren tsafi. Sun gina masallacin juma’a na farko a Kano.

• Sun karfafi yada addinin. Sun bude kofar shigowar malamai daga wurare. Lokacin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa an yi gyare- gyare da yawa don su dace da musulunci (1463-1499). Wannan ya taimaka wajen yada da karfafa addinin a kasar Kano. Bayan wasu shekaru da irin wadannan gyare-gyare da aka yi sai mutane suka fara komawa al’adun su na jahilci, da sabo kamar tsafi da shan giya, da sauran su. Sarakuna kuma sai zalunci. A lokacin ne aka samu Kalmar nan da ake cewa, ai abu kaza ya shige shanun sarki, watau kwace. Sarakunan kan kwace shanu ko gida ko gona ko ya mata ko bayi da sauran su, sai kawai ace sun shie shanun sarki. Watau sun zamo na sarki ko an yarda ko a yarda ba. Wannan yanayi sai Suna wa’azi a kan cewa a dawo kan hanyar Allah da manzon Sa. Shugabanni su daina zalunci, talakawa su ji tsoron Allah. Wanda ya fi shahara a cikin wadannan malamai a kasar Hausa a lokacin shi ne wani Bafulatani daga kabilar Fulani ta Torankawa, dan kasar Gobir. Shehu Usman Dan Malam Muhammadu Fodiyo. A farkon karni na goma-sha-tara sai Sarkin Gobir Yumfa ya fahimci idan aka kyale malaman nan musamman Dan Fodio, to babu shakka talakawa za su yi bore. Don haka sai ya fitar da wadannan dokoki:- Ba a yarda mabiya Shehu su dinga rawani ba, haka kuma mata su daina lullubi. (An lura ne rawani da lullubi na bayyana yawan musulmi masu goyon bayan Danfodio). Duk wanda aka musuluntar ya koma addinin sa. Baako ina aka yarda a yi wa’azi ba. Fassarar da Dan-Fodio da jama’ar sa suka yi ga wadannan dokoki shi ne, sarki ya nemi fito-na-fito da musulmi ma su neman a gyara zaman al’umma. Don haka sai suka yi shawarar yin hijira daga inda su ke, watau Degel suka nufi Gudu. Aka yi sansani a can. A nan ne jama’a suka yiwa Shehu Dan Fodio mubaya’a haifar da malamai masu wa’azi ya a matsayin kwamandan yaki kuma shugaba (Amiril- Muminina). an A shekara ta 1804 aka gwabza yaki tsakanin mutanen Yumfa da musulmi karkashin Shehu Usmanu Danfodio.

Nasara ta tabbata ga musulmi da musulunci, Aka rushe sarakunan Gobir aka kafa tsari mai bin tafarkin addinin musulunci dodar.

Nasarar su Shehu ta haifar da:- Tsoro a zukatan sarakunan Hausa baki dayan su da makotan su, domin Gobir ita ake gani a matsayin ma fi karfin mayaka.

Ta karfafi sauran jagororin musulmi masu s sha’awar kawo sauyi.

• Ta daukaki Shehu da jama’arsa. Sai ya dauki S shugabancin dukkan musulmi a kasar hausa da makotan ta. Haka kuma Shehu Usman ya karfafi malamai ta hanyar aika wasiku dukkanin kasashen Hausa, yana kira gare su, su tashi, su daukaka Kalmar Allah. Su share shakiyanci da zalunci, wannan ya kara zaburar da malamai a ko’ina a kasar Hausa. Sai suka fara shirye- shirye. Ya kyautu a nan mu dan tuna wa mai karatu cewa ita Kano ta bambanta da sauran kasashen Hausa wajen maganar addinin musulunci. Sarakunanta sun yi irin na su kokari wajen karfafa addinin musulunci. Ba za a manta da kokarin sarkin Kano Tsamiya da magajinsa Sarki …

(( mu hadu a kashi na uku ))

Leave a Reply