Arewahausatv latest news

Labaran duniya

buhari nashan suka sabi da nunawa mata wariya

shugaban nigeriya muhammadu buhari na shan suka tun bayan da ya sanya sunan mace guda a jerin sunayen da ya sanya wa wasu tashoshin jiragen kasa.

a ranar litinin ne shugaban ya sanyawa tashoshin jiragen kasa 23 sunan wasu fiitattun mutane da sukayi wani abin bajinta a kasa ko kuma suka bayar da wata gudunmuwa ga kasa

daga cikin sunayen da ya sa harda sunayen tsoffi n shugabannin kasar da ministoci da kuma mutumin da ya karbi kyautar nobel wole soyinka.

to saidai kuma ya sanya sunan fun milayo ransome kuti, wata mai fafutuka kuma mahaifiyar mawakinnan marigayi fele kuti a cikin daya daga cikin tashar jiragen kasan da ya sanyawa suna.

wasu mutane a shafukan sada zumunta sun danganta wannan radin suna da yadda shugaban yayi a 2019 lokacin da ya nada ministoci 43, inda 7 ne kawai daga cikin su mata.

ma abota shafukan zumunta sunnce akwai mata da dana da ya kamata a karraman a sanya sunansu a wasu tashoshin jirgin kasan kamar, stella adadevoh, likitar da ta mutu a yayin da take kokari wajen kare yaduwar cutar Ebola.

sai kuma dora akunyii, wadda ta sha gwagwarmaya wajen hana shigo da jabun magunguna cikin kasar da ta mutu a 2014.

tsohon sanata a nigeriya shehu sani, ya tambayi shugaban kasar da ya sanya sunan tashar jirgin kasa ta kaduna sunan matukiyar jirgin yakin nan da ta rasu makonni biyu da suka wuce, tolulope arotile.

,, kuci gaba da bibiyar mu domin samun wasun labaran duniyav ,,

Leave a Reply