Arewahausatv latest news

Koyarwa

yadda ake bude Gmail account cikin sauki

koyarwa kan yadda zaka bude Gmail account cikin sauki

barkan ku da shigowa wannan shafi na koyarwa kan yadda zakayi amfani da yanar gizo cikin sauki da yadda zaka samu kudi dashi cikin sauki,

a wannan koyarwar zan koyar daku yadda mutum zai bude Gmail account a wayar sa ko computer cikin sauki, domin ince wannan koyarwa tana da mahimmanci sosai da sosai da sosai domin nan gaba koyarwar da zamuyi dole sai ya kasance kana da Gmail account domin ince indai kana amfani da yanar gizo dole sai ka bukaci wannan Gmail account din, misali idan zaka bude Youtube channel ko wani application ko banki ko makaranta dole sai an tambaye ka wannan Gmail din da dai sauran abubuwa masu mahimmanci dole idan zakayi amfani dasu sai kana da Gmail

wannan koyarwa ce kan yadda zaka bude Gmail account nan gaba kuma zamuyi koyarwa kan yadda mutum zai bude YOUTUBE CHANNNEL cikin sauki da yadda zai samu kudi da ita da dai sauran su kuci gaba da bibiyar mu a wannan shafi mai suna Arewahausatv domin samun wasu koyarwar cikin harshen hausa,

ka karanta wannan koyarwar daga farko zuwa karshe zaka ga yadda zaka bude Gmail account cikin sauki da inganci..

da farko zaka shiga izuwa wannan adireshin zaka ga ya bude ma wannan form din na kasa kamar haka Create your google account here

Create your google account here

sai ka cike wannan form din da suka nuna ma kamar yadda nayi acikin wannan hoton na kasa, inda suka sa { first name } zaka sa sunan sa na farko wanda kake amfani dashi, sannan inda suka sa { last name } shi kuma zaka sa sunan mahaifin ka, kamar yadda nasa, misali { first name = ilimi, last name = fasaha, sai inda suka sa { username } shi kuma zaka zabi sunan da kakeson ka ringa amfani dashi a matsayin gmail account dinka, kamar yadda nasa nawa misali {{ ilimifasaha2020@gmail.com }] kaima sai ka zabi irin sunan da kake so sai kasa, kada ka manta idan kasa sunan ka hada da lambobi kamar guda uku ko hudu sabi da idan ka sa sunan sa kawai zasu iya cema wani ya rikawa budewa da irin sunan ka don haka sai ka chanza wani sunan wanda ba wanda ya taba budewa dashi amfanin kara lambobi a gaban sunan da ka zaba zai taimaka ma wajan kasancewa kai kadai ne mai irin sunan ba wanda ya taba budewa da sunan, sai wajan da akasa {{ password }} zaka sa makullin sirrin da kakeson ka ringa amfani dashi wajan bude Gmail din da ka bude misali idan ka shiga youtube suka ce kasa Gmail dinka bayan ka sa Gmail din zasu ce kasa password dinsa to wannan shine password din da zaka sa wanda kasa a alokacin da zaka bude Gmail din, sai ka zabi password din da kakeso ka tabbata yawan password din yakai lambobi ko harufa guda takwas 8, bayan kasa password zaka ga a gaban password din sunsa {{ confirm }} sai ka kara rubuta password din irin wanda kasa a wajan da sukasa password bayan ka sa sai ka duba kasa zaka ga ansa {{ Next }} sai ka danna alamar next din zai kara bude ma wani shafin da zaka karasa cike form din bude gmail din …

bayan ka danna alamar next din zai kara bude ma wani shafin inda zaka sa lambar wayar ka wacce kake amfani da ita,

wani lokacin zasu iya baka zabi suce ba sai ka sa lambar wayar ka ba wani kuma lokacin zasu ce dole sai ka sa lambar wayar, ka tabbata lambar da zaka sa tana aiki kuma tana kan wayar ka ko kusa da kai domin zasu turo ma da lambobi na sirri wanda zasu bukaci ka sa su

bayan kasa lambobin sirrin sai ka danna alamar next kaci gaba da cike form din, zasu kara budema wani shafin kamar haka

a wajan da suka sa {{ recovery email address [ optional ] }} sun baka zabi ne na zaka iya sa wani gmail accound din na abokin ka ko dan uwanka domin ko da ace nan gaba ka manta password dinka zaka iya amfani da wannan gmail din da ka sa a wajan, idan akwai gmail din da ka sani na abokin ka ko wani a gidan ku zaka iya sawa idan kuma ba wanda ka sani to ba sai ka sa ba sai ka barshi yadda yake kamar yadda nima na barshi ban cike ba.

a kasa kuma zaka cike kwanan watan da aka haifeka da shekarar da aka haifeka

inda akasa {{ month }} zaka zabi a watan da aka haifeka sai ka danna ka sa sunan watan kamar yadda na sa nawa April, sannan a wajan da aka sa {{ Day }} zaka sa ranar da aka haifeka ma’ana nawa ga wata kamar yadda nasa an haifeni uku 3 ga wata , inda kuma akasa {{ year }} zaka sa a wacce shekara aka haifeka kamar yadda nasa an haifeni a shekarar 1996 kai ma sai ka zabi a shekarar da aka haifeka sai ka cike ,

a kasa kuma inda aka sa {{ Gender }} zaka zabi jinsin ka ma’ana kai namiji ne ko mace, idan namiji ne kai sai kasa [[ Male ]] idan kuma macece ke sai kisa [[ Female ]] i dan kuma baka san fadar jinsin ka sai kasa [[ rather not ]]

bayan ka gama cike jinsin ka sai ka duba kasa zaka ga ansa [[ Next ]] sai ka danna alamar next ne sai kara budema wani shafin inda ka gama bude Gmail account dinka kenan, bayan ka danna zai budema shafi kamar haka sai ka duba can kasan shafin da ya bude ma

sai ka duba kasan wannan shafin zaka ga inda aka sa [[ i agree ]] sai ka danna alamar da aka sa i agree

bayan ka danna i agree zai budema wani shafin inda zai ma barka da zuwa ma’ana ka bude gmail account dinka sannan zai nunama zaka iya amfani dashi a ko ina a fadin yanar gizo wajan bude duk wani application kamar su youtube da sauran su

kada ka manta zaka iya amfani da gmail dinka ako ina a yanar gizo inda akace kasa [[ Email }} to zaka iya sa wannan wanda ka bude da password dinsa sannan ka samu takarda ka rubuta Gmail dinka da password dinsa domin gudun kada ka manta

wannan shine Gmail din da muka bude acikin wannan koyarwar

Gmail = [[ ilimifasaha2020@gmail.com ]]

password = [[ 98*****6*** ]]

kaima sai ka sami takadda ka rubuta kamar haka gudun kada ka manta ko da nan gaba zaka yi amfani dashi wajan bude YOUTUBE CHANNEL kamar yadda zamuyi koyarwa cikin harshen hausa kan yadda mutum zai bude youtube channel to ka ga idan zaka bude youtube channel zaka iya budewa da wannan wanda ka bude yanzu ba sai ka kara bude wani ba.

mungode sosai da sosai da bibiyar mu da kuke kada ku manta kuyi subscribing din channel din mu a youtube mai suna [[ usamancy ]] domin samun wasu koyarwar acikin video cikin sauki da kuma sanin dabaru kan yadda zaka yi amfani da yanar gizo da yadda zaka sami kudi a yanar gizo dukka zaka iya samu acikin wannan channel din mai suna [[ usamancy ]] insha allah

Leave a Reply