Arewahausatv latest news

Koyarwa

Yadda ake bude youtube channel da yadda ake samun kudi da ita

Acikin wannan koyarwar zanyi bayani dalla dalla kan yadda zaka bude youtube channel da yadda ake samun kudi da ita a duk wata

Kamar yadda kuka sani ana iya samun kudi a youtube idan kana da channel

Idan kana da channel ka dora video akai a duk wata youtube din zasu duba suga adadin mutanen da suka kalli tallan da suka sa ma a channel dinka idan ka samu kudi sunkai dala dari $100 zasu fara turama kudi. Zuwa bankin ka a duk kasar da kake a duniya idan kuma baka samu dala yakai dari ba 100 dole sai ka jira zuwa wani watan sannan zasu hada ma da wanda ka samu a watan da ya wuce in basu kai dala dari ba 100

Ana iya samun kudi a youtube sosai da sosai da sosai kamar dai yadda na fada ya danganta da adadin mutanan da suke bibiyar shafinka da adadin tallan da suka gani ko suka danna a acikin videos din da kasa a channel din naka

Kafin ka bude youtube channel ana bukatar ace kana da Gmail account, idan baka dashi nayi koyarwa ta musamman kan yadda zaka bude Gmail account cikin sauki zaka iya dubawa channel din ( usamancy ) a youtube domin ganin koyarwa kan yadda zaka bude gmail account acikin video

Sannan kafin a fara biyan ka kudi a youtube dole sai channel dinka ta samu subscribers 1000 sannan sun kalli a kalla videon da ka dora a channel dinka a kalla sau awa dubu hudu 4000

In ka samu adadin abubuwan da suke so a channel dinka sannan zasu fara sama talla a channel dinka in suka sama talla acikin channel dinka daganan zaka fara samun kudi da channel din cikin sauki

Kamar dai yadda kuka sani dole duk abinda akace na neman kudi ne to dole fa sai ka samu yana da wuya, kamar dai youtube ko ince samun kudi a yanar gizo

Samun kudi a yanar gizo ba abune mai sauki ba amma in ka jure har zuwa lokacin da zaka fara samun kudin to fa in ka fara samu komai zai zo ma da sauki don haka dole sai ka jure sannan kayi aiki tukuru kafin ka fara samun kudi

Idan kana da youtube channel baa yadda kaje kayi downloading din fina finai a internet ba kazo ka sa a channel dinka, domin doka ne a youtube inkasa videon da ba naka ba to fa zasu iya goge ma channel ko kuma du dakatar da ka na wani lokaci, sannan ya danganta da videon da ka dora akan channel din ya danganta da mai videon wani mai videon zai ce idan ka sa videon sa a youtube channel dinka to duk kudin da ka samu wajan sa zaije kai ba abinda zaka samu domin videon mallakin sa ne, wani kuma zai ce bai yadda ba don haka zasu iya goge ma channel ko su dakatar dakai na wani lokaci mai tsawo sannan su dawo da kai,

Nayi koyarwa dalla dalla da yin bayani sosai acikin video wanda na sa a youtube zaka iya dubawa youtube channel din ( usamancy ) domin kallon ( koyarwa kan yadda ake bude youtube channel da yadda ake samu kudi da ita ) acikin video

Kada ka manta ka kalli videon daga farko har karshe domin kallon koyarwar cikin sauki

Ka danna adireshinnan mai suna koyarwa kan yadda ake bude youtube channel da yadda ake samun kudi da ita

Kayi subscribing din channel din mu domin kallon wasu koyarwar cikin sauki

Leave a Reply